“Babu Shakka Ku Masu Son Zaman Lafiya Ne”- Inji Sakatariyar Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ga Almajiran Sheikh Zakzaky a Abuja

“Babu Shakka Ku Masu Son Zaman Lafiya Ne”- Inji Sakatariyar Kungiyar Kare Hakkin Bil’Adama ga Almajiran Sheikh Zakzaky a Abuja
“Babu shakka ku masu son zaman lafiya ne”, cewar Sakatariyar Hukumar kare hakin Bil’Adama a birnin Abuja, a yayin gangamin kiran #A saki Sheikh Ibraheem Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenatudden Ibraheem a lokacin tunawa da cikar shekaru 2 cur, tun bayan kazamin kisan kiyashin Zaria.
Sakatariyar, Mrs. Orti Ovrawa ta furta haka ne a yayin da tazo amasar koken dubban masu gangamin a harabar Ofishinta dake birnin Abuja.
A yayin takaitattun jawabanta, ta bayyana gamsuwarta ka’in da tsari na zaman lafiya da kiyaye doka-da-oda na mabiya Sheikh Ibraheem Al-Zakzaky wanda gwamnatin Nigeria ka ci gaba da tsare shi tare da mai dakinsa.
Mrs. Orta ta kara da cewa, “Lallai mun shaida yadda kuke kuke fitowa neman hakkokinku cikin tsari da lumana. Wannan fitowa taku ta yau, ita lallai ta kasance cikin tsari da lumana. Kuma mai kira zuwa gareku da ku ci gaba da neman wadannan hakkoki naku cikin tsari da lumana.
A ranakun 12 zuwa 14 ga watan Disambar banan ne dai dubban ‘yan’uwa Musulmi Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky ne suka yi dafifi zuwa birnin na Abuja domin tunawa da cikar shekar 2 cur, da kazamin kisan kiyashin Zariya(wanda Sojoji suka kashe al’ummar kasar mabiya Sheikh Zakzaky fiye da mutum 1000), da kuma ci gaba da kiran #A saki Sheikh din da mai dakinsa tare da sauran wadanda jami’an tsaron kasar ke ci gaba da tsare su bisa taka umarnin Kotu.
Da farko dai bayan isar dubban mabiyan zuwa harabar ta Ofishin kare hakkin bil’Adama dake Abuja, Jami’an hukumar basu saurari masu muzahar ba, a dalilin da yasa suka yanke hukunci su zauna a harabar Offishin hukumar na tsawon sa’o’i, kafin daga bisani Jami’an suka fito domin sauraren koken na dubban masu Muzaharar.
Mrs. Ovrawa dai ta saurari masu koken ta isar da alhininta da kuma kira a garesu da su ci gaba da bin hakkokin su bisa tsari da bin doka-da-oda da aka san su da ita.
Latsa wannan uslubin dake kasa domin ya kaika zuwa amintaccen shafin #Free_Zakzaky_Campaign_Committee domin samun sauran labarai da harshen Turanci.
_details here_👇🏽

“You are most certainly peaceful people” – Human Rights Commission tells IMN


Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google photo

You are commenting using your Google account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s